هناك كثيرٌ من الأمور التي ينبغي للمسلم الجديد أن يتعلمها عن الإسلام، وأهمها أجوبة الأسئلة الثلاثة التي سيُسأل عنها كل من يموت: مَن ربُّك؟ ما دينك؟ مَن نبيُّك؟ وهذا الكُتَيِّب اللطيف يعرض أجوبة هذه الأسئلة بأسلوب ميسَّر جذَّاب؛ ليكون هاديًا للمسلم الجديد في رحلته المباركة نحو مرضاة الله والجنة.
WASU TUSHEN DA BABU MAKAWA SAI
AN SANSU:
Idan kashiga Addinin Musulunci to lallai cewa akwai wasu al’amuran da yake wajaba akanka ka nemi sanin su, da kuma sanin su, daga wannan akwai sanin amsar tambayoyi uku muhimmai waɗanda za’a tambayi kowane mutum akansu bayan mutuwa, waɗanda suke iyakance makomar sa ta dindindin, ko ةdai zuwa Aljanna ko kuma zuwa wuta, sune:
- Waye Ubangijin ka
- Menene Addinin ka
- Waye Annabin ka